Isa ga babban shafi
Najeriya - Tsaro

An kashe Malami da Dalibi a wani kwaleji dake Lagos

Rahotanni daga Lagos dake Najeriya na cewa wasu ‘yan bindiga sun harbe wani malamin jami’a da dalibi a kwalejin Ilimi na Michael Otedole dake karamar hukumar Epe a jihar.

Kwalejin Ilimi na Michael Otedole dake karamar hukumar Epe dake jihar Lagos a Najeriya.
Kwalejin Ilimi na Michael Otedole dake karamar hukumar Epe dake jihar Lagos a Najeriya. © Photo credit: Jority Omo-Agbeke
Talla

Rahotanni suka ce an kashe malamin mai suna Ahmed Saheed  a yankin Poka yayin da dalibin mai suna Razak Bakare ya gamu da ajalinsa cikin dakin kwanan dalibai.

Majiyar ‘yan sanda tace mummunar lamarin ya faru ne sa’o’i 48 tsakaninsu da juna, wato tsakanin ranakun Laraba da kuma Jumma’a.

Wani dan majalisa da ba saraken yankin sun tabbatar da aukuwar lamarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.