Isa ga babban shafi
Najeriya

Gobara ta tafka barna a fitacciyar kasuwar kayayyakin gyaran mota dake Legas

Rahotanni daga jihar Lega a tarayyar Najeriya sun ce wata gobara da ta tashi da tsakar dare ta lalata kayayaki na miliyoyin naira a fitacciyar kasuwar kayayyakin kayan gyara na motoci mai suna Ladipo.

Wani gini mai hawa 3 da gobara ta tashi cikinsa a kasuwar Ladipo dake birnin Legas.
Wani gini mai hawa 3 da gobara ta tashi cikinsa a kasuwar Ladipo dake birnin Legas. © Daily Trust
Talla

Bayanai sun ce, ta fara tashi ne daga wani katafaren shagon sana’ar kafinta a kasuwar ta Ladipo, daga bangaren layin Mushin, daga bisani kuma gobarar ta bazu zuwa wani dakin ajiyar kayayyakin gyaran mota

Bincike ya nuna cewar tartsatsin wutar lantarki ne ya haddasa tashin gobarar da lakume dukiya mai tarin yawa.

Shugaban gudanarwar Hukumar Agajin Gaggawa ta Najeriya NEMA a yankin Kudu maso Yammacin kasar, Ibrahim Farinloye, ya bayyana cewa gobarar wadda ta shafar wani bene mai hawa uku ta ci gaba da ruruwa har zuwa safiyar ranar Litinin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.