Isa ga babban shafi
Najeriya

Gobara ta tafka barna dalilin fashewar bututun mai a Legas

Rahotanni daga birnin Lagos dake Najeriya sun ce an samu fashewar bututun mai a unguwar Abule Ado abinda yayi sanadiyar barkewar gobarar da ta kama gidaje da kuma makarantar ‘Yam mata yau da safe.

Wani bangare na yankin Ijegun dake birnin Lagos a kudancin Najeriya, bayan da aka samu fashewar bututun mai. 15/5/2008.
Wani bangare na yankin Ijegun dake birnin Lagos a kudancin Najeriya, bayan da aka samu fashewar bututun mai. 15/5/2008. REUTERS/George Esrir
Talla

Shaidun gani da ido da kuma bidiyon da aka watsa a kafofin sada zumunta sun nuna yadda hayaki ya tirnike sararin samaniya sakamakon cin wutar da kuma kururuwar jama’a dake neman dauki daga jama’a da masu aikin kashe gobara.

Kakakin hukumar agajin gaggawa na Jihar Lagos Nosa Okunbor ya tabbatar da barkewar gobarar, inda yace jami’an su sun ruga domin kai dauki ga jama’a da kuma kashe wutar.

An ruwaito cewar kamfanin man NNPC ya bada umurnin kashe injinan sa domin bada damar kashe wutar, yayin da jami’an ta suka ruga inda aka aka samu hadarin.

Wannan dai ba shine karo na farko da ake samun gobara sakamakon fashewar bututun mai a wannan unguwa ba, domin ko a watan Janairu mutane 3 suka mutu lokacin da aka samu gobarar wanda aka danganta da masu fasa bututun mai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.