Isa ga babban shafi
RUSHEWAR-BENE

An gano karin mutanen 6 da rai a benen da ya rushe a Lagos - Sanwo-Olu

Gwamnan Jihar Lagos dake Najeriya Babajide Sanwo-Olu yace anyi nasarar ceto karin mutane 6 da ran su, kwanaki 5 bayan rushewar bene mai hawa 21 a unguwar Ikoyi, abinda ya kawo adadin mutanen da aka ceto da ran su zuwa 15.

Gwamnan Lagos Babajide Sanwo-Olu da takwaran sa na jihar Nasarawa Abdullahi Sule da jagoran Jam'iyyar APC Bola Ahmed Tinubu lokacin da suka ziyarci inda bene mai hawa 21 ya rufta a Ikoyi
Gwamnan Lagos Babajide Sanwo-Olu da takwaran sa na jihar Nasarawa Abdullahi Sule da jagoran Jam'iyyar APC Bola Ahmed Tinubu lokacin da suka ziyarci inda bene mai hawa 21 ya rufta a Ikoyi © LASG
Talla

Yayin da ya ziyarci wurin da aka samu hadarin tare da jagoran Jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu da kuma Gwamnan Jihar Nasarawa Abdullahi Sule, Sanwo-Olu yace ya zuwa yanzu an tabbatar da mutuwar mutane 42, yayin da wasu daga cikin wadanda aka ceto kuma ke asibitin Falomo inda ake kula da su.

Gwamnan yace sun dauki cikakken bayanan mutanen da hadarin ya ritsa da su, kuma sun fara tantance gawarwakin su tare da taimakon ‘yan uwa da iyalan su domin yi musu jana’iza.

Gwamna Sanwo-Olu da Abdullahi Sule tare da Bola Ahmed Tinubu a wurin da ake aikin ceto
Gwamna Sanwo-Olu da Abdullahi Sule tare da Bola Ahmed Tinubu a wurin da ake aikin ceto © LASG

Sanwo-Olu yace za’a gudanar da gwajin kwayar halitta akan wadanda aka kasa tantance su domin gano ‘yan uwan su.

Gwamnan ya kuma sanar da cewar sun ware kudade domin taimakawa ‘yan uwan wadanda suka mutu domin gudanar da jana’iza ga masu bukata, yayin da gwamnatin sa ta dauki nauyin tallafawa wadanda suka samu raunuka domin sake fasalin rayuwar su bayan hadarin.

Sanwo-Olu yace zasu ci gaba da aikin ceto har sai an kwashe burabuzan ginin da ya rushe baki daya, yayin da suke dakon rahoton kwamitin binciken da suka kafa domin gano musabbabin abinda ya haddasa hadarin da kuma gano ko an samu sakaci daga hukumomin da aikin ginin ya rataya akan su.

Hotan ginin da ya rsuhe daga sama
Hotan ginin da ya rsuhe daga sama Benson Ibeabuchi AFP/Archivos

A ranar litinin da ta gabata ne ginin mai hawa 21 dake unguwar Ikoyi ya fadi da tsakar rana akan ma’aikata da kuma wasu mutane da dama cikin su harda wanda ya mallaki ginin.

Rahotanni farko sun ce an saba ka’idar ginin wajen kaucewa tanade tanaden da aka tsara, abinda ya sa gwamnan Lagos Babajide Sanwo-Olu ya dakatar da shugaban hukumar kula da gine gine da kuma kafa kwamitin bincike.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.