Isa ga babban shafi
#EndSars

Gangamin cika shekara guda da zanga-zangar EndSars a Najeriya

Masu zanga-zangar neman kawo karshin cin zarafi da ‘yan sanda ke yi da akayi wa lakabi da Endsars sun fito  a wasu biranen kasar, domin tunawa da cigar zanga-zangar shekara guda da abinda suka kira amfani da karfin da jami’an tsaro suka yi wajen murkushe su a bara.

Wasu masu zanga-zangar bacin rai kan cin zarafin da wasu 'yan sanda ke yi a Najeriya.
Wasu masu zanga-zangar bacin rai kan cin zarafin da wasu 'yan sanda ke yi a Najeriya. Temilade Adelaja/Reuters
Talla

Duk da gargadin da rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta yi cewa ba za ta lamunci duk wani nau’i na zanga -zanga a jihar ba, masu zanga -zangar a ranar Laraba sun mamaye kofar shingen karbar harajin ababen hawa Lekki don gabatar da korafinsu kan cin zarafin‘ yan sanda da kisan gilla kan matasa marasa laifi a kasar.

Masu zanga -zangar suna amfani da motocinsu don yin suna ihu suna wajen neman ingantacciyar Najeriya.

Enugu da Abuja

A Enugu da birnin tarayyar Najeriya Abuja, rahotanni sun ce masu zanga -zangar sun mamaye manyan tituna, dauke da alluna daban -daban tare da ihun suna cewa #Endsars da kuma zaluncin 'yan sanda a Najeriya”.

Sowore

A Abuja, an ga Omoyele Sowore, tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AAC, kuma mamallakin jaridar intanet Sahara Reporters, cikin masu zanga-zangar.

An kame wasu masu zanga-zanga

Ya zuwa lokacin wallafa wannan labari jami’an tsaro sun cafke akalla masu zanga -zanga akalla 2 a Lekki dake Lagos.

Daya daga cikin wadanda aka kama ya yi ikirarin cewa dan jarida ne shi, yayin da aka ga dayan na dauke da kwalin mai rubutun zanga-zangar, sai dai wasu rahotanni sun ce mutum 6.

A cewar mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Legas, CSP Adekunle Ajisebutu,‘Yan sanda sun haramta zanga -zanga a jihar saboda: “gujewa sake barkewar munanan tarzoma irin wanda aka gani a shekarar da ta gabata inda aka kashe wasu‘ yan Najeriya marasa laifi ciki har da jami’an ‘yan sanda, kwashe ganima da lalata kaddarori.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.