Isa ga babban shafi
#EndSars

An bada belin masu zang-zangar Endsars 40 da aka tsare a Lagas

Wata Kotu a Birnin Lagos dake Najeriya ta bada belin masu zanga zangar da aka kama a karshen mako, dake bukatar ganin an yi adalci kan mutanen da suke zargin an kashe bara lokacin zanga zangar adawa da cin zarafin da ake yiwa jami’an 'Yan sanda.

Yan sanda Najeriya a hanyar lekki dake Lagos
Yan sanda Najeriya a hanyar lekki dake Lagos REUTERS/Temilade Adelaja
Talla

Lauyan masu zanga zangar Akeem Fadun yace kotu ta bukaci wadanda aka kama su 40 da su biya naira dubu 100-100 a matsayin kudin beli, saboda za’a ci gaba da gudanar da bincike a kansu kan karya dokokin korona da kuma neman tada hankali.

Gungun ‘yan Endsars dake adawa da rundunar ‘yan sanda ta Sars sun sake kiran zanga-zangar ce ranar Asabar, bayan da kwamiti da gwamnatin jihar Lagos ya nada bayan rikicin da ya barke a bara, ya amince da a sake bude shingen biyan harajin ababen hawa na Lekki Tall gate.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.