Isa ga babban shafi
NAJERIA-SARAUTA

Hukumomin Neja sun sanar da rasuwar Sarkin Sudan na Kontagora

Hukumomin Jihar Neja dake Najeriya sun sanar da rasuwar Sarkin Sudan na Kontagora, Alhaji Saidu Umaru Namaska wanda ya kwashe shekaru 47 a karagar mulki.

Sarkin Sudan na Kontagora - Alh Saidu Namaska
Sarkin Sudan na Kontagora - Alh Saidu Namaska © Daily Trust
Talla

Bayanai sun ce Sarkin Sudan ya rasu ne yana da shekaru 84 a duniya, kuma yana daya daga cikin Sarakunan arewacin Najeriya da suka fi dadewa akan karagar mulki.

Mutuwar Sarkin na zuwa ne watanni 3 bayan kisan da ‘Yan bindiga suka yiwa ‘dan sa Alhaji Bashar Saidu Namaska a gonar sa tare da wasu ma’aikatan sa.

Gwamnatin Jihar Neja ta bayyana kaduwar ta da rashin Basaraken wanda ya taka gagarumar rawa wajen ci gaban Masarautar sa da kuma Jihar baki daya.

Sakataren Gwamnatin Jihar Alhaji Ahmed Ibrahim Matane ya bayyana Sarkin a matsayin wanda yafi kowa dadewa a karagar mulki, yayin da ya mika sakon ta’aziyar sa ga Masarautar Kontagora da jama’ar ta da kuma Jihar Neja baki daya.

Matane yace Gwamnan Jihar Abubakar Sani Bello ya aike da sakon ta’aziyar rasuwar Sarkin wanda ya taimaka wajen zaman lafiyar Jihar.

An dai haifi Sarkin Sudan na Kontagora Alhaji Saidu Namaska ne a ranar 31 ga watan Disambar shekarar 1937, kuma ya zama Sarkin Sudan a shekarar 1974 a matsayin Sarki na 6.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.