Isa ga babban shafi
Najeriya

Masarautar Shinkafi ta yamutse saboda nadin Fani Kayode

Yanzu haka wani rikici ya barke a Masarautar Shinkafi da ke jihar Zamfarar Najeriya sakamakon nadin sarautar da aka yi wa Femi Fani-Kayode a matsayin daya daga cikin masu bada shawara ko kuma ‘dan Majalisar Sarki.

Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama na Nejeriya Femi Fani-Kayode
Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama na Nejeriya Femi Fani-Kayode vanguardngr
Talla

Rahotanni sun ce, Sarkin Shinkafi Alhaji Muhammadu Makwashe Isa ya bai wa tsohon Ministan Sufurin Jiragen Saman Najeriyar wannan mukamin sarautar wanda ya haifar da cece-kuce a ciki da wajen masarautar saboda sukar da Kayode ke yi wa 'yan arewacin kasar.

Wannan ya sa wasu daga cikin masu rike da sarautar gargajiya a masarautar ta Shinkafi suka sanar da ajiye mukamansu saboda nuna rashin amincewa da wannan nadi da suka bayyana a matsayin karan-tsaye ga masarautar shinkafi da kuma arewacin Najeriya baki daya.

Daga cikin wadanda suka ajiye mukamansu kuma suka bayyana shirin zuwa kotu domin kalubalantar nadin da aka yi wa tsohon ministan, har da Sarkin Shanun Shinkafi, Dr. Suleiman Shuaibu Shinkafi kamar yadda ya shaidawa Sashen Hausa na RFI.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakkiyar hirarsa da Bashir Ibrahim Idris.

03:27

Masarautar Shinkafi ta yamutse saboda nadin Fani Kayode

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.