Isa ga babban shafi
NAJERIYA-SIYASA

Buhari ya kori wasu ministocin sa guda 2

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kori wasu ministocin sa guda biyu da suka hada da ministan noma Alhaji Sabo Nanono da takwaran san a wutar lantarki Saleh Mamman.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari © Nigeria presidency
Talla

Mai magana da yawun shugaban Femi Adeshina ya tabbatar da korar manyan jami’an guda biyu wadanda ke rike da manyan ma’aikatu a karkashin gwamnatin Buharin, amma ba tare da bayyana dalilin yin haka ba.

Adeshina yace an maye gurbin su da ministan muhalli Dr Mohammed Mahmood Abubakar da kuma ministan kasa a ma'aikatar ayyuka da gidaje Abubakar Aliyu.

Korar ministocin biyu na zuwa ne bayan shekaru biyu da nada su sakamakon sake zaben shugaban kasar a shekarar 2019.

Wadannan ministoci sune na farko da shugaban ya kora tun bayan sake rantsar da shi a karagar mulki.

Sabo Nanono ya fito ne daga Jihar Kano, yayin da Saleh Mamman ya fito daga Jihar Taraba.

Wasu manoman shinkafa a Najeriya
Wasu manoman shinkafa a Najeriya IFAD

Yan Najeriya sun dade sona korafi dangane da yadda ake tafiyar da ma’aikatar noman kasar a karkashin tsohon ministan duk da ci gaban da gwamnati ke ikrari da shi na habaka noma da kiwo.

Yau dokar hana kiwo a kudancin Najeriya ke fara aiki, wani babban koma baya da ake dangantawa da gwamnatin Muhammadu Buhari.

A bangaren samar da wutar lantarki kuma, Yan Najeriya sun dade suna gabatar da korafi akan yadda ake tatsar su kudade ba tare da samun isashiyar wutar da suke samu ba.

Rahotanni sun ce yau aka shirya fara aiki da Karin farashin wutar a Najeriya duk da karancin ta a wasu sassa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.