Isa ga babban shafi
ABINCI-MAI GUBA

Mutane 20 sun mutu a Sokoto sakamakon cin abinci mai guba

Akalla mutane 20 aka tabbatar da mutuwar su a wani gari da ake kira Danbargaje dake karamar hukumar Issa a Jihar Sokoton Najeriya sakamakon cin abinci mai guba.

Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal
Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal dailypost
Talla

Rahotanni sun ce wata mata ce ta sanya gishirin lalle a miya cikin kuskure lokacin da take girki abinda yayi sanadiyar mutuwar mutanen Yan gida guda.

Kansilan dake wakiltar mazabar Muazu Kabir wanda ke cikin shugabannin da suka ziyarci inda lamarin ya faru ya shaida mana cewar hadarin ya auku ne cikin kuskure.

Wannan hadari ya jefa al’ummar Yankin dake karamar hukumar Issa cikin rudani sakamakon iftila’in wanda ke zuwa a daidai lokacin da ake fama da cutar amai da gudawa a yankin.

A makon jiya hukumomin Jihar Sokoto sun ce akalla mutane 23 suka mutu sakamakon barkewar cutar ami da gudawa, wanda ya kama mutane da dama, yayin da aka sanar da mutuwar 30 a Zamfara da kuma 60 a Katsina.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.