Isa ga babban shafi
Najeriya - Zamfara

Mazauna kauyukan Shinkafi na fuskantar barazanar karin hare-haren 'yan bindiga

Rahotanni daga arewacin Najeriya na cewa mazaunan wasu yankunan karamar hukumar Shinkafi da ke jihar Zamfara da dama na cikin fargaba, kwanaki biyu bayan da wasu ‘yan bindiga dake karkashin jagorancin Turji, wani sanannen shugaban‘ yan fashin daji, suka afkawa yankin.

Hoto domin misalin 'yan bindiga a Najeriya.
Hoto domin misalin 'yan bindiga a Najeriya. REUTERS/Goran Tomasevic/File Photo
Talla

Yan bindigar dauke da muggan makamai sun afkawa kauyukan karamar hukumar ta Shinkafi da dama ne domin daukar fansar kame mahaifin Turji da jami’an tsaron Najeriya suka yi, inda suka sace mutane ciki har da matafiya akalla 150 kamar yadda jaridar Daily Trust dake Najeriya ta ruwaito.

Kauyukan da gungun ‘yan bindigar suka afkawa tun a ranar Juma’a, sun hada da Kurya, Kware, Marisuwa, Keta, Badarawa, Maberaya.

Bayanai daga jihar ta Zamfara kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito sun ce ‘yan bindigar sun lissafa wasu karin kauyuka akalla 32 da za su kaiwa farmaki, cikin wasikar da jagoransu Turji ya aike da ita inda ya bukaci su fice daga muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.