Isa ga babban shafi
Najeriya-Korona

Tsanantar cutar korona ta tilasta kulle jami'ar Lagos a Najeriya

Hukumar gudanarwar Jami’ar Lagos da ke Najeriya ta bukaci daliban ta da ke zama a dakunan makarantar da su fice sakamakon samun wasu dalibai da ke dauke da cutar korona.

Wasu dalibai a harabar Jami'ar Lagos.
Wasu dalibai a harabar Jami'ar Lagos. homelandnewsng
Talla

Mataimakin shugaban Jami’ar Farfesa Oluwatoyin Ogundipe ya sanar da matakin bayan wani taron gaggawa da ya jagoran ta yau domin nazarin da ake ciki.

Oluwatoyin ya ce taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar ya yanke hukuncin dakatar da karatu har zuwa ranar 26 ga wannan watan da za a ci gaba da kafofin bidiyo.

Tuni asibitin Jami’ar ya sanar da fuskantar abinda ake kira zagaye na 3 na annobar koronar, kwana guda bayan gwamnatin Lagos ta yi gargadi akai.

A karshen makon da ya gabata Gwamnan Lagos Babajide Sanwo-Olu ya sanar da jama’ar Jihar cewar ana fuskantar dawowar annobar karo na 3 sakamakon karuwar masu harbuwa da ita da aka gani wanda ya tashi daga sama da kashi 1 zuwa sama da kashi 6 da rabi a ranar 8 ga wannan watan.

Ita ma Jami’ar Lagos ta fuskanci karuwar masu zuwa da alamun cutar, abinda ya sa aka sanar da hukumomin ta domin daukar mataki.

Sashen kula da lafiya na Jami’ar ya ce ya na daukar matakan da suka dace domin kare lafiyar dalibai da ma’aikatan dake cikin jami’ar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.