Isa ga babban shafi
Najeriya - IPOB

Wata kungiyar kabilar Igbo ta bukaci gaggauta sakin Nnamdi Kanu

Wata Kungiyar kwararru 'Yan Kabilar Igbo ta bukaci Gwamnatin Najeriya da ta gaggauta sakin shugaban haramcaciyar kungiyar IPOB dake fafutukar kafa kasar Biafra Nnamdi Kanu, yayin da ta yi Allah wadai da kashe wasu ‘yayan kungiyar sa ta IPOB a Kudu maso Gabashin kasar.

Hoton shugaban 'yan awaren yankin kudancin Najeriya Nnamdi Kanu a wani gida dake Umuahia,  a shekarar 2019.
Hoton shugaban 'yan awaren yankin kudancin Najeriya Nnamdi Kanu a wani gida dake Umuahia, a shekarar 2019. AFP - CRISTINA ALDEHUELA
Talla

Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya Farfesa Chukwuma Soludo ya gabatar da matsayin kungiyar a ganawar da suka yi da manema labarai inda yake cewa.

"Muna bukatar gaggauta sakin Nnamdi Kanu da abokan tafiyar sa da duk wadanda aka tsare saboda ra’ayoyin su"

Kungiyar tace, hakan na a matsayin wani bangare na shirin hada kan jama’ar kasa da kuma gina sabuwar Najeriya.

Soludo ya kara da cewa, Akwai mahawarar dake gudana a tsakanin 'Yan Najeriya dangane da batun Biafra, kuma akwai wasu 'Yan kabilar Igbo kamar sauran 'Yan Najeriya da basu amince da manufofin Nnamdi Kanu ba, ko hanyar da yake bi, amma ya dace a bayyana cewar babu wani dan Najeriya da ya dace a masa abinda aka yiwa Nnamdi Kanu da abokan tafiyar sa.

Tsere Kanu

Cikin makon da ya gabata Gwamnatin Najeriya ta sanar da kame jagoran masu fafutukar kafa kasar Biafra ta IPOB Nnamdi Kanu wanda ya tsere daga kasar tun cikin shekarar 2017 bayan da aka bada belinsa daga shari’ar da ya ke fuskanta kan cin amanar kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.