Isa ga babban shafi
Najeriya - IPOB

Najeriya ta zayyana wa kasashen duniya laifukan Nnamdi Kanu

Gwamnatin Najeriya ta ce jagoran haramtacciyar kungiyar IPOB mai neman kasar Biafra Nnamdi Kanu, ya haddasa kashe mutane akalla 60 tare da lalata dukiya mai yawan, yayin hare-hare fiye da 50 da mabiyansa suka kai a sassan yankin kudu maso gabashi da kuma kudu maso kudancin kasar.

Jagoran masu fafutukar kafa Biafra a kudancin Najeriya Nnamdi Kanu, lokacin da ya gurfana a gaban kotu a shekarar 20215
Jagoran masu fafutukar kafa Biafra a kudancin Najeriya Nnamdi Kanu, lokacin da ya gurfana a gaban kotu a shekarar 20215 AP - AP Photo
Talla

Daga cikin jerin ta’adin Nnamdi Kanu da gwamnatin Najeriya ta zayyana cikin wasikun da ta aikewa jakadun kasashen yammacin Turai akwai hare-haren da mabiyansa suka kai tsakanin 26 watan Janairu zuwa 19 ga Afrilun da ya gabata a jihar Abia inda suka kasha ‘yan sanda 6, sai a Akwa Ibom inda ‘ya’yan haramtacciyar kungiyar IPOB suka kashe mutane 25 ciki har da jami’an tsaro yayin hare-haren da suka kaddamar a sassan jihar tsakanin 27 ga watan Janairu zuwa 19 ga watan Afrilu.

Wasikar gwamnatin Najeriya ta kara da cewar mabiyan Nnamdi Kanu sun kuma kashe ‘yan sanda da soja daya a jihar Cross River a farkon watan Maris, yayin da kuma tsakanin watan Janairu zuwa tsakiyar Afrilu, suka kasha mutane 11 ciki har da jami’in tsaro a garin Onitcha dake jihar Delta.

Wasikar gwamnatin Tarayya

Aikewa da wasiku zuwa ga Jakadun kasashen yammacin Turan kan ta’adin mabiyan Nnamdi Kanu ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin Najeriya ke bayyana damuwa kan yadda hukumomin wasu kasashen ketaren ke goyon bayan masu tayar da kayar bayan masu neman ballewar da suke yi, ta hanyar baiwa jagoran nasu damar watsa shirye-shiryen tunzura barkewar rikici ta kafar rediyo.

Tserewar Kanu

Kanu da ya tsere daga Najeriya a shekarar 2017 bayan belin shi da kotu ta bayar, ya sake gurfana gaban babbar kotun Najeriya dake Abuja A ranar Talata, bayan kamo shi da jami’an tsaron Najeriya suka yi daga ketare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.