Isa ga babban shafi
NAJERIYA-TATTALIN ARZIKI

Amaechi ya bukaci hukuncin kisa akan masu yiwa sufuri zagon kasa

Ministan sufurin Najeriya Rotimi Amaechi ya bada shawarar sanya hukuncin kisa akan mutanen dake kwance layin jirgin kasa da gwamnati ke shimfidawa domin inganta sufurin jiragen kasa a fadin kasar.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari REUTERS - Siphiwe Sibeko
Talla

Yayin da yake tsokaci akan matakan da gwamnati ke dauka na sanya na’urorin da zasu dakile satar karafan hanyar jiragen da ake shimfidawa, ministan yace ana bukatar doka mai tsanani akan wadanda aka samu da laifin kwance layin dogon saboda illar da zai yi wajen harkar sufurin da kuma haifar da hadura.

Amaechi yace kamfanin jiragen kasan Najeriya yayi asarar akalla karafan layin dogo dubu 15 akan hanyar Abuja zuwa Kaduna kawai a cikin shekaru 5 da suka gabata.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yana amsa gaisuwa daga jama'a
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yana amsa gaisuwa daga jama'a © Buhari Sallau

Ministan yace wannan ya sa suka kaddamar da shirin sanya na’urorin da zasu taimaka wajen hana satar a hanyoyin jiragen kasa da kuma kadarorin hukumar sufurin baki daya.

Ko a makwannin da suka gabata jami’an Yan Sanda sun kama wasu mutane da aka gansu suna kwance layin jirgin akan hanyar Lagos zuwa Ibadan.

Sabon tashar jiragen Lagos
Sabon tashar jiragen Lagos © Buhari Sallau

Gwamnatin Najeriya na kokarin farfado da sufurin jiragen kasa a fadin kasar amma kuma wasu na yiwa shirin zagon kasa wajen sace karafan da ake shimfidawa jiragen suna tafiya akan su.

A watan jiya shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da sufurin jiragen sama na zamani da gwamnatin sa ta kamala aikin sa akan hanyar Lagos zuwa Ibadan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.