Rikicin Boko Haram ya hana manoma fiye da dubu 65 zuwa gonakinsu - FAO
Hukumar Bunkasa Noma ta Majalisar Dinkin Duniya FAO, ta yi gargadi game da karancin abinci a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.
Wallafawa ranar:
FAO ta ce matsalar Boko Haram ta hana manoma kimanin dubu 65 da 800 samun gudanar da ayyukan gona a yankin.
Wakilin FAO a Najeriya, Fred Kafeero ne ya bayyana haka yayin bikin kaddamar da ayyukan noman rani na wannan shekara a Maiduguri.
Rahoto kan halin da noma ke ciki a Arewa maso Gabashin Najeriyar na zuwa ne adaidai lokacin da mazauna karamar Hukumar Kala Balge a Jihar Barno ke kokawa kan yadda Giwaye suka addabi ayyukansu na noma, kamar yadda Kaumi Ali Ngalama ya shaidawa sashin Hausa na RFI.
NIGERIA-2021-06-24-KAUMI
Yankin Arewa maso Gabashin Najeriya dai na daga cikin yankunan da manomansu suka amfana da shirin tallafawa bunkasar ayyukan nom ana Ancho Borrower da aka kaddamar a karkashin jagorancin babban bankin kasar CBN fiye da shekaru 3 da suka gabata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu