Isa ga babban shafi
Najeriya-MSF

MSF ta koka kan barazanar da karuwar rikici ke yi ga ayyukan jinkai a Zamfara

Kungiyar likitocin kasa da kasa ta MSF ta bayyana damuwa kan yadda karuwar tashe-tashen hankula a jihar Zamfara ta yankin Arewa Maso gabashin Najeriya ke kokarin dakile shirin kai agaji da dauki ga al’ummar da ke cikin mawuyacin hali.

Wani sansanin 'yan gudun hijirar da hare-haren 'yan bindiga ya tilastawa barin muhallansu a karamar hukumar Anka dake jihar Zamfara.
Wani sansanin 'yan gudun hijirar da hare-haren 'yan bindiga ya tilastawa barin muhallansu a karamar hukumar Anka dake jihar Zamfara. © MSF/Abayomi Akande
Talla

Kungiyar ta MSF cikin sanarwar da ta ke fitarwa yau Alhamis, ta ce matsalolin lafiya na ci gaba da ta’azzara a yankin wanda ke bukatar agaji, yayinda karuwar rashin tsaro ke barazana ga ayyukan kai daukin.

Zamfara da makwabtanta wadanda suka shafe tsawon shekaru suna fama da rikice rikice masu alaka da kabilanci ciki har da na makiyaya da Manoma, kafin daga baya ya juye zuwa hare-haren ‘yan bindiga da ke da nasaba da albarkatun karkashin kasa, kana ya sauya salo zuwa sace-sace lalata kadarorin gwamnati da garkuwa da mutane don fansa da kuma kashe kashen babu gaira babu dalili.

Kungiyar ta MSF ta ce daga watan Janairu zuwa Aprilun da ya gabata ta yi nasarar bai wa kananan yara dubu 10 da 300 kulawa a cutuka masu alaka da karancin sinadarai masu gina jiki, da kyanda da zazzabin cizon sauro da sauran cutukan da ke barazana ga lafiyar yara.

Sai dai sanarwar ta MSF ta ruwaito Dr Godwin Emundanohwo na cewa kalubalen lafiyar yankin ya haura da kimanin kashi 54, wanda alamu ke nuna yiwuwar ninkuwar matsalolin lafiyar da yankin ke fuskanta idan aka kwatanta da wanda aka gani kwatankwacin wannan lokacin a bara.

MSF ta ci gaba da cewa, yankunan da rikicin ya dabaibaye na bukatar agajin abinci, ruwan sha da kuma rigakafin cutuka baya ga magunguna, sai dai karuwar matsala tsaro na ci gaba da zama babbar barazana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.