Isa ga babban shafi
Najeriya - Amnesty

Amnesty ta sake caccakar shugabannin Najeriya kan gaza kare rayukan 'yan kasar

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta zargi gwamnatin Najeriya da gazawa wajen daukar matakan kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasar, gazawar da ta Amnestyn tace tana karawa miyagu kwarin gwiwar cigaba da tafka ta’asa san ransu.

Tambarin kungiyar kare hakkin bil'ada ta Amnesty International
Tambarin kungiyar kare hakkin bil'ada ta Amnesty International @សហការី
Talla

Amnesty International ta bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ta fitar yayin bikin cikar ta shekaru 60 da kafuwa.

A cewar darakatan kungiyar ta kare hakkin dan adam a Najeriya Ossai Ojigho, kasar ta dade da tarihin fuskantar matsalar kasa magance take hakkin dan adam, kare rayukan da dukiyar ‘yan kasar, tauye ‘yancin fadin albarkacin baki da kuma rashin shugabanci na gari tun shekarar 1967.

Amnesty ta kara da cewar cigaba da salwantar da rayukan jama’a ta hanyar yi musu kisan gilla da kuma sakacin gwamnati wajen murkushe miyagun tare da hukunta su, na cigaba da zama barazana babba ga hakkin rayuwa a Najeriya.

Wasu masu zanga-zangar korafi ga gwamnati a birnin Legas dake kudancin Najeriya. 11/1/2012.
Wasu masu zanga-zangar korafi ga gwamnati a birnin Legas dake kudancin Najeriya. 11/1/2012. Tolu Ogunlesi/Open access

Kungiyar ta kuma koka kan yadda ‘yancin bayyana korafi ko ra’ayi ke fuskantar koma baya a kasar ta Najeriya, sakamakon dakile damar mutane ta gudanar da zanga-zangar nuna bacin rai kan lamurran dake damunsu.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da Amnesty International ke wallafa rahoton dake caccakar gwamnatin Najeriya ba domin jan hankalinta kan kura-kuran da take tafkawa, yayin da su kuma hukumomin Najeriyar ke maidawa kungiyar martanin kare kansu daga zarge-zargen da take musu, gami da yin watsi da wasu rahotannin da suke bayyanawa a matsayin marasa tushe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.