Isa ga babban shafi
Najeriya - 'Yan bindiga

Majalisa na bukatar ɗaurin shekaru 15 ga masu biyan ƙudin fansa

Majalisar Dattawa ta kammala karatu na biyu a kan dokar yanke hukuncin daurin shekara 15 ga duk wanda ya biya kudin fansa ga ’yan bindiga domin ceto wani da suka yi garkuwa da shi, da kuma wanda ya karbi kudin fansa.

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Ahmad Lawan a ofishinsa dake Majalisar, 2 ga watan Afrilun 2021
Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Ahmad Lawan a ofishinsa dake Majalisar, 2 ga watan Afrilun 2021 © Ahmad Lawan Twitter
Talla

Sanata Ezenwa Francis Onyewuchi ne ya gabatar da kudirin na 2021 mai taken 'magance ayyukan ta'addanci.

Da yake jagorantar muhawara kan kudurin, dan majalisar ya ce, "dokar ta'addanci ta 2013 tana bukatar gyara don haramta biyan kudin fansa ga masu satar mutane domin sakin duk wani wanda aka sace ko tsare shi bisa kuskure.

A cewar dan majalisar, kudirin dokar na neman maye gurbin sashi na 14 na Babban Dokar a matsayin wani sabon sashi kamar haka:

"Duk wanda ya tura kudade, ya biya ko kuma ya hada baki da wani mai satar mutane ko kuma ɗan ta'adda don karbar kuɗin fansa da niyyar don sakin wani wanda aka sace ko aka tsare ko ɗaure shi to ya aikata babban laifi kuma zai iya ɗaukar hukuncin ɗaurin shekaru 15. "

Ɗan majalisar ya ƙara da cewa yanzu satar mutane ta zama babban kasuwancin da ke kawo kudi mai yawa cikin sauri, yana mai cewa, "yanzu haka ya kasance mafi munin ta'addanci da ake aikatawa wanda kuma ke ƙara girma a kasar."

Ya ce yadda ake yawan satar mutane a Najeriya ya jefa ƴan ƙasar cikin tsoro da fargaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.