Legas ta gabatar da kananan motocin sufuri 500 bayan haram ta Babura
Gwamnatin Jihar Lagos dake Najeriya ta dauki matakin farko na kawar da 'Yan okada ko masu hayar Babura da masu Keke Napep daga aikin sufuri a birnin, wajen gabatar da kananan motocin sufuri 500 da zasu dinga shiga yankuna 286 na birnin, yayin da manyan motocin safa na BRT kuma za su cigaba da aiki a manyan tituna.
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:30
Yayin bikin kaddamar da sabbin motocin, Gwamnan Jihar Babajide Sanwo-Olu yace wadannan motoci 500 mataki ne na farko na fara gwajin shirin wanda suke saran kara su zuwa 5,000 nan gaba kadan.
Gwamna Sanwo-Olu yace:
Abinda muke yi shine ingantawa da kuma tabbatar da kare lafiyar jama’a da dukiyoyin jama’ar mu. Burinmu shine aiwatar da shirin samar da sufuri mai inganci da kuma kyau da zai maye gurbin wanda ake da shi na okada wajen biyan bukata daga bangaren motocin FLM da muke magana akai.
Gwamnan ya kara da cewar sun dauki matakin ne domin kare lafiya da dukiyoyin jama’a. "Muna bukatar jama’ar mu su samu zabi da kuma fahimtar yadda kowanne daga cikin wadannan hanyoyi za suyi aiki kafin muyi amfani da babbar bulala, wato haramci baki daya da muke magana akai."
Ra'ayoyi dai sun banbanta ga mazauna birnin da suka saba amfani da da wadannan hanyoyin sufuri na babura da keke Napep, wadanda akasari suka nuna rashin jin dadi, kan wannan mataki, yayin da wasu suka yaba da mataki.
Yayin su kuma masu wannan sana'a ta Achaba suke bukatan gwamnatin jihar da ta kawo dauki, domin babu wata sana'a da suka rike.
Tuni gwamnatin Jihar ta bayyana yadda sabon shirin sufurin zai yi aiki da kuma hanyoyi 286 da zasu ci gajiyar shirin baki daya.
Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraron cikekken rahoto da kuma ra'ayoyin wasu da Bashir Ibrahim Idris ya hada mana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu