Yadda wata mujami'ar kiristoci ta tallafa wa musulmai da kayan sallah a Kaduna
A Najeriya, yayin da ake shirin gudanar da bukukuwan Sallah karama, Wata Mujami'a a jihar Kaduna ta rabawa marayu 100 maza da mata kayan Sallah domin faranta ma su rai.
Wallafawa ranar:
A duk shekara musulmi a fadin duniya na gudanar da bikin sallah bayan kammala azumin watan Ramadan, Sai dai Marayu na shiga cikin halin kunci sakamakon rashin iyaye da zasu yi masu hidima musammam ma a irin wannan lokaci.
A bisa la'akari da irin wannan halin kunci da marayu ke shiga yasa wata Mujami'a a jihar Kaduna karkashin jagorancun Fasto Yohana Buru rabawa marayu maza da mata guda 100 kayan sawa domin ta faranta ma su rai adaidai lokacin da za'a gudanar da bikin sallah.
NIGERIA-KADUNA-AMINU-SADO-2021-05-12
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu