Isa ga babban shafi
Najeriya - Abuja

Najeriya: 'Yan fashi sun yi yunkurin aika aika a kusa da fadar shugaban kasa

‘Yan fashi sun yi yunkurin aika aika a gidan shugaban ma'aikatan fadar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari dake kusa da fadar gwamnatin tarayyar kasar a birnin Abuja.

Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari daga farko a bangaren hagu, yayin halartar wani taron ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari daga farko a bangaren hagu, yayin halartar wani taron ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari. © Twitter / @MBuhari
Talla

Kafofin yada labarai da dama sun ruwaito cewar baya ga gidan shugaban ma’aikatan a fadar gwamnatin Najeriyar Farfesa Ibrahim Gambari, ‘yan fashin ko barayi sun kuma yi yunkurin shiga gidan wani babban ma’aikacin fadar shugaban kasar, said ai basu samu nasara ba.

Cikin sanarwar da ya wallafa a shafinsa na twitter kakakin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Malam Garba ya tabbatar da aukuwar lamarin da ya auku da misalin karfe 3 na daren jiya Litinin, wanda ya bayyana a matsayin ganganci.

Garba Shehu ya kara da cewar na’urar boye ta daukar hoto ta gano wani dan fashin da a ranar Alhamis yayi yunkurin shiga gidan Maikano Abdullahi wani babban ma'aikaci a fadar shugaban Najeriyar kuma ‘yan sanda na aikinsu.

Lamarin na zuwa a daidai lokacin da shugaban najeriya Muhammadu Buhari ke shan matsin lamba kan yadda matsalar rashin tsaro ta addabi sassan kasar, duk da kokarin da gwamnatinsa ke cewa tana yi wajen kawo karshen matsalar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.