Isa ga babban shafi
Najeriya - Tattalin Arziki

Buhari ya kafa kwamitin bincikar shugabar hukumar NPA bayan dakatar da ita

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ba da umurnin bincikar shugabar hukumar kula da tashoshin jiragen ruwan kasar ta NPA, Hadiza Bala Usman.

Hadiza Bala Usman, shugabar hukumar kula da tashoshin jiragen ruwan Najeriya da aka dakatar.
Hadiza Bala Usman, shugabar hukumar kula da tashoshin jiragen ruwan Najeriya da aka dakatar. © The Guardian Nigeria
Talla

Sanarwar da kakakin Buhari Malam Garba Shehu ya wallafa ta shafinsa na Twitter a daren Alhamis, ta kuma ce shugaban ya umurci shugabar hukumar ta NPA da ta sauka a mukaminta yayin gudanar da binciken.

“Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da shawarar da ma’aikatar sufuri karkashin jagoranci Rotimi Amaechi ta bayar, kan a kafa kwamiti don ya binciki shugabannin hukumar ta NPA.” Sanarawar Garba Shehu ta ce.

Sai dai sanarwar ba ta ambaci laifukan da ake zargi ko tuhumar Hadiza Bala Usman da su ba.

Gabanin kafa kwamitin binciken, rahotanni sun ruwaito cewa an dakatar da Hadiza Bala Usaman, kuma Fadar shugaban kasar ta ce an nada Mohammed Koko a matsayin mukaddashin hukumar.

“Kwamitin binciken zai samu jagorancin Darektan fannin kula da harkokin sufurin ruwa na ma’aikatar sufurin, yayin da mataimakin darekta na bangaren shari’a zai zama sakatare.”

A cewar Garba Shehu, nan gaba za a nada sauran mamabobin kwamitin binciken.

A shekarar 2016 Buhari ya nada Hadiza Bala Usman, a matsayin shugabar hukumar ta NPA.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.