Isa ga babban shafi
Najeriya - Sadarwa

Kotu ta dakatar da shirin katse layukan sadarwar dubban 'yan Najeriya

Wata babbar kotun Najeriya dake zamanta a birnin Legas ta haramtawa gwamnatin kasar aiwatar da matakin katse layukan sadarwar da aka gaza hada su da lambar katin dan kasa.

Wasu masu sayar da katunan layin sadarwar kamfanin MTN a birnin Legas da ke tarayyar Najeriya.
Wasu masu sayar da katunan layin sadarwar kamfanin MTN a birnin Legas da ke tarayyar Najeriya. AP - Sunday Alamba
Talla

Ranar 6 ga watan Afrilun dake tafe gwamnatin Najeriyar ta hannun ma’aikatar tad a sadarwa ta ayyana a matsayin lokacin da za ta rufe layukan sadarawar da suka gaza cika ka’idar.

Tsohon mataimakin kungiyar lauyoyin Najeriya mai kuma fafutukar kare hakkin dan adam Monday Ubani ne ya shigar da kara gaban babbar kotun, inda ya kalubalanci shirin katse layukan dubban ‘yanb Najeriyar tare da neman kara wa’adin hada layukan sadarwar da lambobin na katin dan kasa.

Matakin kayyade wa’adin sake rijistar layukan dai ya sanya dubban ‘yan Najeriya yin tururuwa zuwa ofisoshin hukumar yin rijistar katin dan kasa domin samun hada layukansu da lambobin da ake bukata, abinda ya janyo karya dokokin yaki da annobar Korona, musamman na hana cinkoson jama’a.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.