Isa ga babban shafi
Najeriya

Obasanjo ya ce Buhari na biyan diyya ga masu garkuwa da mutane

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya zargi shugaba Muhammadu Buhari da biyan 'yan bindiga masu garkuwa da mutane makudan kudade a matsayin diyya.

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo
Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo REUTERS/Joe Penney
Talla

Obasanjo ya shaida wa tawagar wasu kwararru 'yan kabilar Tiv cewar  gwamnatin Goodluck Jonathan da wannan mai ci ta Buhari duk suna biyan diyya ga 'yan bindiga.

Tsohon shugaban ya bukaci gwamnatin Najeriya da ta fito da wani tsari wanda zai magance wannan matsala ta masu garkuwa da mutane da Yan bindiga maimakon biyan diyya.

Sai dai kuma tsohon shugaban yace yaki da matsalar tsaro na bukatar lallashi da kuma duka ga wadanda suka ki bada kai.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito tsohon shugaban na cewa wasu mutane na kokarin tintibar Yan bindigar da zummar shiga tsakani domin ganin an ceto rayukan wadanda akayi garkuwa da su, amma daukar matsayin cewar za’a dinga biyan diyya a koda yaushe ba zai haifar da da mai ido ba.

Jaridar tace Obasanjo ya taka rawa sosai wajen sakin daliban kwalejin Kaduna da aka sako yau bayan kwashe wajen wata biyu ana garkuwa da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.