Isa ga babban shafi

Obasanjo ya bukaci Buhari da ya hana jami'an tsaro kisan masu zanga-zanga

Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya dakatar da sojoji da kuma sauran jami’an tsaro daga amfani da karfin da ya wuce kima akan masu zanga zanga.

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo
Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo REUTERS/Joe Penney
Talla

A sanarwar da ya rabawa manema labarai, Obasanjo ya bi sahun fitattun shugabannin duniya irin su tsohon mataimakin shugaban Amurka Joe Biden da tsohuwar Sakatariyar harkokin waje Hillary Clinton wajen Allah wadai da yadda sojojin suka afkawa masu zanga zangar.

Yayin da ya bukaci masu zanga zangar su kai zuciya nesa ya kuma bukaci gwamnati da tayi Nazari kan bukatun su wadanda yake cewa abubuwa ne masu yiwuwa.

Gwamnan Lagos Babajide Sanwo Olu yace babu wanda ya mutu a harbin da sojoji suka yi jiya, sai dai wasu mutane sun samu raunuka kuma ya ziyarce su a asibiti.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.