Isa ga babban shafi
Najeriya - Zamfara

Zan kawo karshen 'yan bindiga a Zamfara cikin kwanaki 4 - Matawalle

Gwamnan jihar Zamfara a Najeriya ya lashi takobin murkushe 'yan bindiga cikin kwanaki hudu tare da kawo karshen muggan ayyukansu a fadin jihar.

Gwamnan jihar Zamfara a Najeriya Bello Matawalle, a cikin ofishinsa dake jihar
Gwamnan jihar Zamfara a Najeriya Bello Matawalle, a cikin ofishinsa dake jihar © Governor Matawalle
Talla

Gwaman Bello Matawalle Muradun ya bayyana haka ne lokacin da ya karbi bakwancin shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC karkashin jagorancin Gwamnan jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu da takwaransa na Jigawa Abubakar Badaru a wani ziyarar jaje da suka kai Gusau.

Gwamna Matawalle ya gargadi 'yan bindiga a jihar da su tuba ko su sauya sheka domin ya tsara sabon tsarin yadda zai tunkari matsalar kalubalen tsaro da jihar ke fuskanta.

Ya ce dakatarwar da ya yi wa wani hakimi a masarautar Shinkafi kwanan nan saboda mu’amala da 'yan ta'adda somin tabi ne, yana mai cewa a cikin kwanaki hudu masu zuwa, zai shawo kan duk wadanda ke sanya rayuwar al’umma da basu ji ba basu gani ba cikin kuncin rayuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.