Isa ga babban shafi
Najeriya

Ai ba'a tsare Buhari ba duk da kiran Jonathan ya yi murabus - Falana

A Najeriya ficeccen Lauyan nan mai kare hakkin dan Adam, Femi Falana, ya yi tir da tsare tsohon Mashawarci na Musamman ga Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, wato Salihu Tanko Yakasai.

Ficeccen Lauyan Najeriya kuma mai kare hakkin dan Adam, Femi Falana,
Ficeccen Lauyan Najeriya kuma mai kare hakkin dan Adam, Femi Falana, falana.jpg
Talla

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta tabbatar da cewar, Tanko Yakasai yana tsare a hannun ta, sai dai ta musanta zargin cewar saboda ya bukaci shugaban kasa Mohammadu Buhari yayi murabus ne saboda tsaro suka kama shi.

A wata sanarwa da ya gabatar a ranar Lahadi, Falana ya ce ana tsare da Salihu ne summun bukumun, saboda kawai ya yi amfani da ‘yancin fadin albarkacin bakinsa kamar yadda sashe na 39 na Kundin Tsarin Mulkin shekarar 1999 ya bashi dama.

Ficeccen lauyan yace, tsakanin shekarar 2013 zuwa 2014, shugabannin jam’iyyar APC, ciki har da Buhari, Asiwaju Bola Tinibu, Malam Nasir El-Rufai da Alhaji Lai Mohammed sun bukaci tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da ya yi murabus.

Kuma babu wanda yaci zarafinsu ko fuskantar wata barazana saboda amfani da 'yancinsu na fadin albarkacin a lokacin.

Babban Lauyan, wanda shi ne Shugaban riko na Gamayyar kungiyoyin yaki da annobar COVID-19 da wasu matsaloli a Najeriya, (ASCAB), ya nuna mamakin dalilin da ya sa aka kama Salihu bayan yawancin kungiyoyin farar hula da shugabannin jam'iyyar APC da na majalisun dokokin tarayya guda biyu duk sun sha kira ga shugaba Buhari ya sauka ko ma a tsige shi saboda halin rashin tsaro da kasar ke ciki.

Falana Yace: "Shawarar magabatan da suka kafa Kundin Tsarin Mulkin da aka amfani da shi yanzu haka, ya baiwa kowa 'yancin faɗin albarkacin baki, wanda dole ne ya haɗa da' yancin yin suka"

Ficeccen lauyan ya bukaci hukumar tsaron ciki gida ta DSS tayi gaggawan sakin tsohon mashawarcin gwamnan kanon ko kuma su gurfanar da shi gaban kuliya idan yana da laifi.

“Dangane da abin da ya gabata, muna neman a gaggauta sakin Mista Tanko-Yankasai dake tsare ba bisa ka’ida ba, ko kuma, idan Jami'an Tsaron na da shaidar cewa wanda ake tsare da shi a siyasance ya aikata wani laifi da doka ta san shi ya kamata a tura shi ga 'yan sanda don gudanar da bincike mai inganci ko ma gurfanar da shi ba tare da wani bata lokaci ba. "

 

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da tabbatar da cewa tsohon mai taimaka wa gwamnan na Kano yana hannunta, ta ce ba don fadin albarkacin baki ta tsare shi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.