'Yan bindiga sun saki daliban Kagara kwanaki 10 bayan yin garkuwa da su
‘Yan bindiga a Najeriya sun saki daliban makarantar sakandaren Kagara 27 da kuma malamansu da wasu ma’aikata 15 da suka sace kwanaki 10 da suka gabata a jihar Neja.
Wallafawa ranar:
A tsakiyar watan Fabarairun da muke gungun ‘yan bindiga sanye da kakin sojoji suka kutsa makarantar sakandaren ta Kagara inda suka yi awon gaba da mutane 42, da suka hada da dalibai 27 da malamai da wasu ma’aikata 15, bayan da suka kashe dalibi guda 1 da yayi kokarin tserewa.
Yayin tabbatar da sakin daliban ta shafinsa na twitter, gwamnan jihar ta Neja Abubakar Sani Bello yace tuni ya karbi bakuncin jumillar mutanen 42 a garin Minna.
Governor Sani Bello of Niger State Receives Government Science Collage Kagara Abductees...Says Government to Put Up a System to Identify Root Causes of Banditry. pic.twitter.com/VrzWcUKcIE
— Governor Niger (@GovNiger) February 27, 2021
Sakin daliban na Kagara na zuwa ne, a yayinda hankula suka tashi a ciki da wajen Najeriyar, biyo bayan sace dalibai 317 da wani gungun ‘yan binidgar suka yi daga makarantar ‘yammata ta Jengebe dake jihar Zamfara, wadanda hukumomin tsaro suka bazama wajen kokarin ceto su.
Tuni dai gwamnatin Zamfara ta bada umarnin rufe ilahirin makarantun kwanan dake jihar, domin dakile yunkurin sake kai farmakin sace dalibai, matakin da ita ma gwamnatin Kano ta dauka, inda ta garkame wasu makarantun kwanan dake kauyukan jihar.
Hare-haren ‘yan binidga da satar mutane a yankin arewa maso yammacin Najeriya na cigaba da yin kamari a baya bayan nan, duk da ikirarin gwamnati na daukar matakan kawo karshen matsalar da suka hada da murkushe barayin da karfin jami’an tsaro, tare da mika musu tayin sulhu a matakan wasu jihohi.
A shekarar bara wasu gungun ‘yan binidgar suka sace dalibai sama da 200 daga makarantar sakandaren kimiyya ta Kankara da ke jihar Katsina, wadanda aka sako su bayan shafe kusan mako guda ana garkuwa da su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu