Isa ga babban shafi
Najeriya

Hukumar DSS ta bankado shirin haddasa rikicin addini a wasu jihohin Najeriya

Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya DSS, ta ce ta bankado makarkashiyar da wasu mugaye ke yi na kokarin haddasa rikicin addini a wasu jihohin arewaci da kuma kudancin kasar.

Jami'an hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya DSS
Jami'an hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya DSS venturesafrica
Talla

Cikin sanarwar da ya fitar a ranar Litinin, Afunanya Peter, jami’in hulda da jama’a na hukumar tsaron ta DSS, yace jihohin da ake shirin kullawa mugun zare sun hada da Kaduna, Kano, Sokoto, Filato, Legas, Oyo, Rivers da kuma wasu jihohin dake yankin kudu maso gabashin Najeriya.

Hukumar tsaron farin kayan ta kuma yi gargadin cewa, akwai yiwuwar kaiwa shugabannin addinai da wuraren ibada farmaki, dan haka kamata yayi jama’a su guji dukkanin lamurran za su tayar da hatsaniya, zalika su gaggauta kaiwa jami’an tsaro mafi kusa tegumi kan dukkanin abinda basu aminta da shi ba.

A yayinda aka samu saukin fuskantar rikice-rikicen addini shekarun baya bayan nan a Najeriya, jami’an tsaron kasar a yanzu sun maida hankali ne wajen kokarin kawo karshen matsalolin tsaron da suka hada da hare-haren ‘yan bindiga da satar mutane don kudin fansa musamman a yankin arewa maso yammaci, sai kuma rikicin Boko Haram a arewa maso gabashin kasar, matsalolin da a baya bayan nan ke karuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.