Isa ga babban shafi
Najeriya

Hukumar DSS ta musanta kama Magu

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS a Najeriya, ta musanta kama mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci ta EFCC Ibrahim Magu.

Wasu jami'an hukumar DSS a Najeriya.
Wasu jami'an hukumar DSS a Najeriya. guardian.ng
Talla

A wata sanarwa da DSS ta rabawa manema labarai, hukumar tace babu gaskiya cikin rahotannin da wasu kafafen yada labarai suka wallafa cewar jami’anta sun kama Magu bisa wasu dalilai da ake alakantawa da laifukan almundahanar kudade.

Cikin wata sanarwa da EFCC ta fitar a baya bayan nan, kakakin hukumar Dele Oyewale yace ba kama Magu aka yi ba, illa kawai shugaban ya bayyana ne a gaban wani kwamitin bincike a fadar gwamnatin Najeriya dake Abuja, domin amsa tambayoyi kan yadda yake tafiyar da ayyukan hukumar.

Rahotanni sun ce ba a baiwa manema labarai damar shiga zauren da shugaban an EFCC Ibrahim Magu ke amsa jerin tambayoyi daga kwamitin binciken a fadar shugaban kasa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.