Isa ga babban shafi
Najeriya

Jami'an DSS sun kame shugaban EFCC Ibrahim Magu

Rahotanni daga Najeriya sun ce jami’an tsaron farin kaya na hukumar DSS, sun kama mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci ta kasar EFCC Ibrahim Magu.

Ibrahim Magu, mukaddashin shugaban hukumar EFCC.
Ibrahim Magu, mukaddashin shugaban hukumar EFCC. Premium Times
Talla

Jaridar Daily Trust da ake wallafa ta a Najeriya ta ruwaito cewar, jami’an na DSS sun yi awon gaba da Magu ne daga hedikawatar hukumar ta EFCC dake Abuja da yammacin yau litinin.

Kamen da aka yiwa Magu na zuwa ne kwanaki kalilan bayan da ministan shari’a Abubakar Malami, ya zargi shugaban na EFCC da wasu laifuka ciki har da karkatar da makudan kudaden satar da aka kwato, tare da neman shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kore shi daga mukaminsa.

Kawo yanzu dai shugaban na EFCC da kuma kakakinsa basu ce komai kan lamarin ba, sai dai a baya shugaban na EFCC ya sha musanta zarge-zargen da ake masa na aikata ba daidai ba, wadanda ya bayyana a matsayin tuggun siyasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.