'Yan Najeriya 9 na neman madafun iko a zaben Amurka
Akalla ‘yan asalin Najeriya mazauna Amurka 9 ne ke takarar neman mukamai daban-daban a babban zaben kasar da ke gudana a yau Talata.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriyar ya ruwaito cewa cikin ‘yan takarar akwai Oye Owolewa, daga jihar Kwara, da ke takarar neman shiga majalisar wakilan Amurka don wakiltar yankin Colombia a karkashin jam’iyyar Democrat, idan kuma yayi nasara zai zama dan Najeriya na farko a majalisar.
Daga cikin manyan manufofin Owolewa mai shaidar digirin digirgir akwai yakar nuna wariyar launi.
Sauran 'yan Najeriyar sun hada da Mista Yomi Faparusi dan asalin jihar Ekiti, da shi ma a matakin tarayyyar ke takarar kujerar dan majalisar dattijai a Amurkan mai wakiltar jihar Tennessee.
Faparusi na da shaidar karatun digirin digirgir a fannin likitanci, kuma daga cikin manufofinsa akwai kare hakkokin ‘yan Najeriya da kuma basu kwarin giwar neman mukaman siyasa a Amurka.
Shi kuwa Yinka Faleti, wani dan Najeriyar daga Lagos, yana neman ofishin sakataren harkokin waje ne a karkashin jam’iyyar adawa ta Democrat a Amurkan daga jihar Missouri.
Faleti na da shaidar karatun digirin farko daga makarantar horas da sojojin Amurka.
A matakin jiha a Amurkan kuwa akwai Paul Akinjo, dan asalin jihar Ondo, wanda ke takarar neman shiga majalisar dokokin jihar California a karkashin jam’iyyar Democrat, kuma Daga cikin manufofinsa akwai bada fifiko ga batutuwan samarwa da mallakar gidaje, sufuri da kuma shige da ficen baki.
Duk dai a matakin jihar a Amurka, Adewunmi Kuforiji na takarar neman kujera a majalisar dokokin jihar Delware ne. Kuforiji na asalin jihar Oyo a Najeriya na da shaidar karatun digiri na 2 a fannin kasuwanci.
Esther Agbaje ita ‘yar Najeriya ce da ke neman kujera a majalisar dokokin jihar Minnesota a Amurkan karkashin jam’iyyar Democrats.
Esther Agbaje kwararriyar Lauya ce da ta samu shaidar digirin farko da na biyu a fannin.
A matakin kananan hukomomi kuwa, ‘yan Najeriyar da ke takara a babban zaben Amurkan sun hada da April Ademiluyi, Ngozi Akubuike da kuma Bejamin Osemenam.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu