Isa ga babban shafi

Kungiyar Ohaneze Ndigbo ta nesanta kanta daga rikicin EndSars a Legas

Kungiyar Dattawan Yan Kabilar Igbo ta Ohaneze Ndigbo ta nesanta kan ta daga kalaman Nnamdi Kanu shugaban kungiyar dake fafutukar kafa kasar Biafra dangane da tarzomar da aka samu a Lagos bayan zanga zangar adawa da cin zarafin jami’an Yan Sandan dake yaki da ‘Yan fashi da makami.

Wasu masu zanga-zangar bacin rai kan cin zarafin da wasu 'yan sanda ke yi a Najeriya.
Wasu masu zanga-zangar bacin rai kan cin zarafin da wasu 'yan sanda ke yi a Najeriya. Temilade Adelaja/Reuters
Talla

Kungiyar ta bayyana kaduwar ta da irin kalaman da Nnamdu Kanu keyi na tinzira jama’a dangane da irin ta’adin da aka samu a birnin Lagos wanda suka ce zai shafi dangantaka tsakanin Yan Kabilar Igbo da Yarbawan dake Jihar.

Shugaban kungiyar John Nwodo ya bayyana kalaman Nnamdi Kanu a matsayin abin takaici wanda ke iya raba kan kabilun Igbo da Yarbawa da aka kwashe shekaru ana dangantaka mai kyau.

Wannan matsayi na kungiyar Ohaneze na zuwa ne bayan da kungiyar Yarbawa ta Apapo O’Odua Koya ta fitar da sanarwa dangane da yadda take zargin Yan Kabilar Igbo da lalata dukiyar jama’a a Lagos.

Nwodo yace sanarwar da kungiyar Yarbawar ta bayar wani yunkuri ne na gwara kan kabilun guda biyu, yayin da ya nesanta rawar da matasan Igbo suka taka a tarzomar da aka samu da zummar lalata tatatlin arzikin Yarbawan dake Lagos.

Shugaban kungiyar yace ba zasu taba bari dangantakar da aka kulla mai dimbin tarihi tsakanin kabilun biyu lokacin Dr Nnamdi Azikiwe da kuma Dim Chukwuemaka Odumegwu Ojukwu ya watse ba.

Nwodo yace sun dada inganta wancan dangantakar da kakannin su suka kulla a shekaru 3 da suka gabata wajen hadin kai tsakanin kungiyar Middle Belt daga Arewa da Ndigbo daga Kudu maso Gabas da Afenifere daga Kudu maso Yamma da kuma PANDEF daga Kudu maso Kudu.

Shugaban kungiyar yace har yanzu suna bakar sun a bukatar ganin an sake fasalin Najeriya ta hanyar tabbatar da adalchi da daidaito.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.