Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Dakta Dikko Umaru Radda kan shirin bunkasa kanana da matsakaitan masana'antu a Najeriya

Wallafawa ranar:

Hukumar bunkasa matsakaita da kananan sana’o’I ta Najeriya SMEDAN, ta ce yanzu haka fanninta ne ke kan gaba wajen samar da ayyukan yi a kasar da kashi 76.5, inda kimanin mutane miliyan 59 da dubu 647, ke cin abinci a fannin.Hukumar ta bayyana wadannan alkaluma ne yayin kaddamar da shirin tallafa wa matasa kusan dubu 1 da 500 a jihohin kasar 11, wanda wasu daga ciki suka hada da, Katsina, Zamfara, Delta, Rivers, sai kuma Legas, inda bikin ya gudana.Nura Ado Suleiman da halarci taron, ya zanta da babban daraktan hukumar bunkasa matsakaita da kananan masana’antun na Najeriya SMEDAN Dr Dikko Umaru Radda.

Bashir Ibrahim Idris
Bashir Ibrahim Idris © RFI
Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.