Isa ga babban shafi
Najeriya-Abuja

'Yan bindiga sun sace mutane da dama a Tungar Maje

Rahotanni daga Najeriya sun ce gungun ‘yan bindiga sun sace mutane kimanin 20 a kauyen Tungar Maje dake makwaftaka da Jihar Niger da kuma Abuja, babban birnin tarayyar kasar.

'Yan bindiga sun sace kimanin mutane 20 a kauyen Tungar Maje dake Najeriya.
'Yan bindiga sun sace kimanin mutane 20 a kauyen Tungar Maje dake Najeriya. Jakarta Globe
Talla

Bayanai sun ce jami’an sintirin sa kai na ‘yan Vigilante sun yi kokarin dakile harin ‘yan bindigar da ba a tantance adadinsu ba, amma suka gaza samun nasara, inda maharan suka tsere da wadanda suka sacen zuwa cikin jihar Niger.

Sai dai yayin karin bayani ga manema labarai kan harin, kakakin rundunar ‘yan sandan birnin Abuja, DSP Ajunguri Manzah yace mutane 10 ‘yan bindigar suka sace, kuma tuni sun samu nasarar ceto biyar daga ciki, zalika suna cigaba da farautar maharan.

A watanniin bayan dai babbar hanyar dake sada Abuja zuwa jihar Kaduna ce tayi kaurin suna wajen fuskantar matsalar satar mutane da ‘yan bindiga ke yi don karbar kudin fansa, sai dai a baya bayan nan matsalar ta soma bayyana a wasu kauyukan dake gaf da babban birnin tarayyar na Najeriya.

Karin jihohin dake fama da matsalar hare-haren ‘yan bindiga sun hada da Sokoto, Zamfara, Katsina, Niger, Nasarawa, da kuma Kaduna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.