Isa ga babban shafi
Najeriya

Mutane 3 sun mutu a hadarin da jirgi mai saukar ungulu yayi a Legas

Kwararrun Jami’an sashin hadurran jirgin sama a Najeriya, sun kaddamar da bincike don gano musababbin hadarin jirgi mai saukar Ungulun da ya rikito kan gidaje a unguwar Opebi dake karamar hukumar Ikeja dake Legas a jiya Juma’a.

Daya daga cikin gidajen da hadarin jirgi mai saukar ungulu ya shafa a unguwar Opebi dake Ikeja a jihar Legas.
Daya daga cikin gidajen da hadarin jirgi mai saukar ungulu ya shafa a unguwar Opebi dake Ikeja a jihar Legas. Radio Nigeria
Talla

Yayin karin bayani kan hadarin, babban daraktan hukumar bada agajin gaggawa a jihar ta Legas LASEMA, Dakta Femi Osanyintolu, yace mutane biyu sun rasa rayukansu, sai dai daga bisani rahotanni sun ce cikon na ukunsu shi ma ya wanda a baya ke halin rai kwakwai mutu kwakwai.

Rahotanni sun ce fasinjan da ba bayyana ko waye shi ba, ya mutu ne a asibitin koyarwa na Jami’ar jihar Legas dake Ikeja.

Bayanai sun ce jirgi mai saukar ungulun da yayi hadari mai suna Bell 206, mallakin kamfanin Quorum Aviation, ya tashi zuwa Legas ne daga birnin Fatakwal, dauke da matuka biyu da fasinja daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.