Isa ga babban shafi

Zulum ya taimakawa 'yan gudun hijira da ya kwaso a Nijar

Daruruwan ‘yan gudun hijiran Najeriya da suka samu mafaka a jamhiriyar Nijar sakamakon hare haren mayakan Boko Haram sun fara komawa gidajensu a karamar hukumar Mobar dake jihar Barno.

Gwamnan Barno Babagana Umara Zulum yayin ziyara yankunan jihar masu mafa da rikicin Boko Haram
Gwamnan Barno Babagana Umara Zulum yayin ziyara yankunan jihar masu mafa da rikicin Boko Haram RFI Hausa
Talla

‘Yan gudun hijrar da suka samu mafaka a sassa daban daban na jamhuriya Nijar sun kwashe sama da shekaru 5 suna gudun hijira domin tsira da rayukan su.

Gwamnan jihar Barno Babagana Umara Zulum ya gana da wasu daga cikin wadanda rikicin ya raba da gidajen su da suka kai 674 a Damasak, inda ya tallafa musu da kayan abinci da kudade domin sake sabuwar rayuwa, yayin da ya duba aikin gina gidaje 1,000 da gwamnati sa keyi a yankin domin rabawa ‘yan gudun hijirar.

Zulum ya kuma bukaci kwamandan sojin dake kula da yankin dda ya taimaka wajen baiwa mutane damar komawa gonakin su domin gudanar da aikin noma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.