Isa ga babban shafi
Najeriya

Akalla mutane dubu 2,500 sun warke daga cutar coronavirus a Najeriya

Cibiyar dakile yaduwar cutuka ta Najeriya NCDC, ta ce an samu adadi mafi yawa na mutanen da gwaji ya tabbatar sun kamu da cutar coronavirus cikin sa’o’i 24 da suka gabata a ranar Laraba, 27 ga watan Mayu.

Wani jami'in lafiya a Najeriya, yayin gwajin cutar coronavirus a birnin Abuja. Afrilu, 2020.
Wani jami'in lafiya a Najeriya, yayin gwajin cutar coronavirus a birnin Abuja. Afrilu, 2020. Reuters/Afolabi Sotunde
Talla

A sabon rahoton da ta wallafa, cibiyar ta NCDC ta ce mutane 389 aka gano suna dauke da cutar coronavirus a tsakanin jihohin Najeriya 22, ciki harda Kogi, wadda a baya annobar bata bulla cikinta.

Legas ce dai ke kan gaba tsakanin jihohin da aka samu sabbin kamuwa da cutar ta coronavirus a ranar Laraba, da mutum 256, adadi mafi yawa da jihar ta gani tun bayan bullar annobar a cikinta.

Sauran jihohin sun hada da Katsina mai mutane 23, Edo 22, Rivers 14, Kano mutane 13, Adamawa da Akwa Ibom na da mutum 11 kowannensu, sai Kaduna da karin mutane 7.

A jihohin Kwara da Nasarawa karin mutane 6-6 suka kamu coronavirus, yayinda Gombe, Filato, Abia, Delta, Benue, Niger, Kogi da kuma Oyo dukkaninsu ke da sabbin mutane bibbiyu da suka kamu. A Borno, Imo, Anambra da Ogun kuma mutane 1-1.

Zuwa yanzu jumillar mutane dubu 2 da 501 suka warke daga annobar coronavirus a Najeriya, daga cikin dubu 8 da 733 da suka kamu, yayinda mutane 254 suka mutu a dalilin cutar, bayan bazuwa zuwa jihohin Najeriya 35 da babban birnin tarayya Abuja. Jihar Cross River ce kawai a yanzu bata annobar ta coronavirus bata shiga ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.