Isa ga babban shafi
Najeriya-Katsina

Matasan Katsina sun yi zanga-zanga kan yawaitar hare-haren 'yan bindiga

Wasu matasa a karamar hukumar Jibia dake Katsinar Najeriya sun gudanar da zanga-zanga a yau, inda suka tare babbar hanyar motar dake zuwa Maradi dake Jamhuriyar Nijar, domin bayyana bacin ransu da yadda gwamnati ta kauda kai ‘yan bindiiga na cigaba da hallaka su.

Yawaitar hare-haren 'yan bindiga ya tilasatawa matasana Katsina gudanar da zanga-zanga. (An yi amfani da wannan hoto a matsayin misali ne kawai)
Yawaitar hare-haren 'yan bindiga ya tilasatawa matasana Katsina gudanar da zanga-zanga. (An yi amfani da wannan hoto a matsayin misali ne kawai) Information Nigeria
Talla

Rahotanni sun ce daruruwan matasan da suka fito daga kauyen Daddara da kauyukan dake makotaka dasu, sun fara zanga zangar ce tun da misalin karfe 8 na safe, inda suka yi amfani da itace da tsoffin tayun mota wajen cinna wuta akan hanyar, abinda ya tilasta dakatar da zirga zirga.

Bayanai sun ce saida shugabannin al’umma da kuma 'yan sanda suka lallashi matasan da rana kafin suka yi hakuri suka janye.

Shugaban kungiyar cigaban 'Daddara' Halilu Buhari ya shaidawa Jaridar Daily Trust da ake wallafawa a Najeriya cewar sun gaji da yadda 'yan bindigar ke cigaba da kashe musu mutane da kuma sace dukiyoyinsu.

Buhari yace kwanaki biyu da suka gabata Yan bindigar sun shiga wani kauye da ake kira 'Yan Gayya, inda suka ci zarafin mata da dama, yayinda suka kuma shiga kauyen Zamdam inda suka yi ta harba na’ura mai fashewa, kafin jama’ar garin suyi kukan kura su kore su.

Al’ummar Jihar Katsina sun dade suna korafi kan irin ukubar da suka samu kansu dangane da hare-haren wadannan 'yan bindiga wadanda suke cin karensu babu babbaka.

Rahotanni sun ce 'yan bindigar sun yi nasarar tarwatsa mutane a kananan hukumomi da dama, abinda ya sa wasu 'yan jihar ke sukar gwamnatin tarayya kan yadda tayi watsi da al’amarinsu wajen samar musu da tsaron da ya dace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.