Isa ga babban shafi
Najeriya-Coronavirus

Mutane 778 sun warke daga cutar coronavirus a Najeriya

Hukumar yaki da yaduwar cutuka ta Najeriya NCDC, tace yawan wadanda suka kamu da cutar coronavirus a kasar a yanzu ya kai dubu 4 da 399, bayan samun karin mutane 248 da suka kamu da cutar a rana 1.

Jami'ar lafiya a Najeriya yayin gwada zafin jikin wata mata.
Jami'ar lafiya a Najeriya yayin gwada zafin jikin wata mata. REUTERS / AFOLABI SOTUNDE
Talla

Alkalumman da hukumar ta NCDC ta fitar sun ce karin mutane 17 annobar ta kashe a jiya Lahadi kadai, wanda karo na farko kenan da aka samu adadi mafi yawa da suka mutu a Najeriya sakamakon cutar ta coronavirus a rana guda.

A bangaren sabbin wadanda da suka kamu da cutar kuwa, hukumar yaki da yaduwar cutukan ta Najeriya tace an sami karin mutanen ne daga jihohin kasar 17, da suka hada da Legas mai mutane 81, Jigawa 35, Borno da Kano kowanne 26-26, Bauchi 20, Abuja 13, Edo 12, sai Sokoto mai mutane 10.

Sauran jihohin sun hada da Zamfara inda aka samu karin mutane 7, Kwara da Kebbi mutane 4-4, Gombe, Taraba, Ogun da Ekiti dukkaninsu 2-2, yayinda Osun da Bayelsa ke da mutum guda-guda.

Sabbin alkalumman hukumar yaki da yaduwar cutuka ta Najeria sun nuna cewa, a yanzu jumillar mutane 778 suka warke daga cikin dubu 4 da 399 da suka kamu da cutar ta coronavirus, yayinda 143 suka mutu.

Har yanzu Legas ke jan ragamar zama inda cutar tafi yaduwa, wadda take da jumillar mutane dubu 1 da 845, biye da ita Kano ce da mutane 602, sai Abuja mai mutane 356, Borno 185, Bauchi 181, Katsina 156, Jigawa 118, Ogun 117, Gombe 112, sai Sokoto mai jumillar mutane 106. A sauran jihohin kuwa zuwa yanzu Kaduna na da jumillar masu cutar corona 98, Edo 79, Zamfara 72, Oyo 64, Osun 39, Kwara 34, Nasarawa 25, Kebbi 24, Rivers 21, sai Filato mai 19.

A jihar Akwa Ibom jumillar mutane 17 suka kamu da cutar coronavirus, Ekiti, Ondo da Taraba 15-15, Yobe 13, Enugu 10, Ebonyi 7, Bayelsa da Niger 6-6, Imo 3, Benue da Abia 2-2, sai Anambra mai mutum 1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.