Isa ga babban shafi
Najeriya-Coronavirus

Adadin masu cutar corona a Najeriya ya zarta dubu 4

Yawan wadanda suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya ya karu zuwa mutane dubu 4 da 151 a daren ranar Asabar, 9 ga watan Mayu, bayan samun karin mutane 239 da suka kamu da cutar a rana 1.

Wata matashiya sanye da takunkumin rufe baki da hanci a kasuwar Wuse dake Abuja. 27/3/2020.
Wata matashiya sanye da takunkumin rufe baki da hanci a kasuwar Wuse dake Abuja. 27/3/2020. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

A rahoton da ta wallafa hukumar yaki da yaduwar cutuka ta Najeriya NCDC daga cikin sabbin mutane da cutar ta kama, 97 daga Legas suke, 44 a Bauchi, 29 a Kano sai kuma 19 a Katsina.

Biye da Katsina, jihar Borno ce da ta samu karin mutane 17 da annobar ta harba, sai Abuja mai mutane 7, Kwara 6, Oyo 5, yayinda Kaduna, Sokoto, da Adamawa ke da sabbin mutane 3-3 da suka kamu da cutar.

Kebbi kuwa, Ogun da kuma Filato karin mutane bibbiyu suka samu, yayinda Ekiti ke da mutum guda.

Sabbin alkalumman hukumar yaki da yaduwar cutukan Najeria sun nuna cewa, a yanzu jumillar mutane 745 suka warke daga cikin dubu 4 da 151 da suka kamu da cutar ta coronavirus, yayinda 128 suka mutu.

Har yanzu Legas ke jan ragamar zama inda cutar tafi yaduwa, bayan samun jumillar wadanda annobar coronavirus din ta kama dubu 1 da 764 kashi 42.5 cikin 100 na adadin wadanda suka kamu a Najeriya.

Kano na da mutane 576, Abuja 343, sai Borno mai 159, Gombe 110, sai Katsina 156, Bauchi 161, Kaduna 98, Ogun 115 sai Sokoto 96, Jigawa kuma 83.

A sauran jihohin Edo na da jumillar mutane 67, a Zamfara 65, Oyo 64, Osun 38, Kwara 30 sai Kebbi da mutane 20. Sauran sun hada da, Akwa Ibom da Delta na mutane 17-17, a Taraba mutane 15 suka kamu, Adamawa da Filato na da 17-17, Ondo 15, , Rivers na da 21, a Yobe mutane 13, Ekiti 13, Nasarawa 25, sai Enugu dake da mutane 10, Niger 6, Bayelsa 5, sai Ebonyi mai mutane 7, mutane 2-2 suka kamu a Abia da Benue, sai Imo mai mutane 3, yayinda a Anambra har yanzu mutum daya ya kamu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.