Isa ga babban shafi
Najeriya-Coronavirus

Yawan wadanda coronavirus ta kama a Najeriya ya zarce dubu 3

Adadin mutanen da suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya ya zarce 3,000 sakamakon samun karin mutane 195 da suka kamu da cutar a jiya laraba, abinda ya kawo adadin zuwa 3,145, yayinda 103 suka mutu.

Wani dan Najeriya sanye da takunkumin rufe hanci da baki a Legas, bayan sassauta dokar hana fita.  4/5/2020.
Wani dan Najeriya sanye da takunkumin rufe hanci da baki a Legas, bayan sassauta dokar hana fita. 4/5/2020. REUTERS/Temilade Adelaja
Talla

Alkalumman da hukumar yaki da cututtuka ta bayar a Najeriya sun nuna cewar daga cikin sabbin mutane 195 da aka samu a jiya Lagos na da 82, Kano 30, Zamfara 19, Sokoto 18, Borno 10, Abuja 9, Oyo 8, Kebbi da Gombe 5-5, Ogun 4, Katsina 3, Kaduna da Adamawa guda-guda.

Rahotan hukumar yace yanzu haka cutar ta shiga Jihohi 34 da kuma Abuja, inda Lagos ke sahun gaba na yawan mutanen da suka kamu da 1,308, sai Kano mai 427, Abuja na da 316, Barno na da 116, Gonbe 103, Katsina da Ogun 95-95, Kaduna da Sokoto 85-85, Bauchi 83 sai Edo mai 65.

Sauran sun hada da Oyo 52, Zamfara 46, Jigawa 39, Osun 37, Kebbi 18, Delta 17, Akwa Ibom 16, Taraba da Adamawa 15-15, Rivers 14, Yobe da Ondo 13-13, Ekiti 12, Nasarawa 11, Enugu 8, Bayelsa da Ebonyi 5-5, Plateau 4, Benue da Imo da Abia bibbiyu sai Anambra mai guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.