Isa ga babban shafi
Coronavirus

Rashin bin doka zai tilastawa gwamnati sake killace 'yan Najeriya - NCDC

Hukumar yaki da yaduwar cutuka ta Najeriya NCDC, tace mai yiwuwa ‘yan kasar su tilastawa gwamanti sake daukar matakin yiwa mutane kulle saboda annobar coronavirus, idan suka cigaba da bijirewa umarnin hukumomi da shawarwarin likitoci kan kauracewa shiga cinkoso.

Yadda cinkoson mutane da ababen hawa ya sake bayyana a birnin Legas bayan sassauta dokar hana fitar da gwamnati ta kafa don yakar annobar coronavirus.
Yadda cinkoson mutane da ababen hawa ya sake bayyana a birnin Legas bayan sassauta dokar hana fitar da gwamnati ta kafa don yakar annobar coronavirus. AFP Photo/PIUS UTOMI EKPEI
Talla

Gargadin shugaban hukumar ta NCDC Dakta Chikwe Ihekweazu a ranar litinin, yazo ne a daidai lokacin da matakin sassauta dokar hana fitar da gwamnatin Najeriya ta kafa a wasu jihohi ya soma aiki a Legas da kuma Abuja.

Sai dai rahotanni sun tabbatar da cewa bayan soma aikin sassaucin dokar hana zirga-zirgar, an samu cinkoson jama’a musamman a bankuna tashoshin mota da kuma kasuwanni, abinda ya saba da umarnin gwamnati da kwararru kan lafiya na gudanar da harkokin yau da kullum cikin taka-tsantsan da kaucewa cincirindo, musamman a wasu yankunan biranen na Legas da Abuja.

Shugaban hukumar yaki da yaduwar cutukan ta Najeriya, ya kuma bayyana matakin bankuna na bude kalilan daga cikin rassan su a matsayin daya daga cikin dalilan da suka haifar da cinkoson jama’ar, abinda yace ka iya mayar da hannun agogo baya, a yakin da kasar ke yi da annobar COVID-19.

Dakta Ihekweazu yace ba shakka a yanayin yadda jama’a suka gudanar da harkokinsu a ranar litinin 4 ga watan Mayu, akwai fargabar samun karin mutane da dama da za su kwashi cutar, sai dai ya shawarci mutane da su koyi gudanar da hada hadarsu cikin kiyaye dokokin likitoci da gwamnati, ko kuma a koma gidan jiya.

Sabbin alkalumman da hukumomin Najeriya suka fitar a daren ranar litinin ya nuna cewar, an samu karin adadin wadanda suka kamu da cutar coronavirus mafi yawa a kasar da mutane 245, ranar da aka saki mara ga mazauna biranin Lagos da Abuja da Ogun.

Alkaluman da hukumar yaki da cututtuka a Najeriya ta bayar sun ce a jiya kawai mutane 245 suka kamu da cutar, yayin da 6 suka mutu, abinda ya kawo adadin wadanda suka kamu da cutar a Najeriya zuwa 2,802, 417 sun warke, 93 sun mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.