Isa ga babban shafi
IMF

Dalilan da suka sanya IMF baiwa Najeriya bashin dala biliyan 3.4

Asusun bada lamuni na duniya IMF ya amince da baiwa Najeriya tallafin bashi na dala biliyan 3 da miliyan 400 a ranar talata 28 ga watan Afrilu.

Shugabar asusun bada lamuni na duniya IMF, Kristalina Georgieva.
Shugabar asusun bada lamuni na duniya IMF, Kristalina Georgieva. REUTERS/Denis Balibouse
Talla

Cikin sanarwar da ya fitar, asusun na IMF yace ya baiwa Najeriya tallafin bashin ne domin taimaka mata wajen yakar cutar coronavirus, da kuma fardo da tattalin arzikinta da tasirin annobar ya tagayyara.

Najeriya ta cika ka’idar shiga jerin kasashen da IMF zai baiwa tallafin bashi ne, la'akari da cewar farashin danyen man da kasar ta dogara dashi ya karye a duniya, sakamakon tasirin annobar coronavirus, hakan tasa kudaden shigar da kasar ke samu ya ragu matuka, duk da cewar a yanzu tafi bukatarsu domin yakar annobar.

Matakin na IMF ya zo ne a dai dai lokacin da majalisar dattijan Najeriya ta amince da bukatar shugaba Muhammadu Buhari na karbar bashin naira biliyan 850 a cikin gida, domin cike gibin kudaden aiwatar ayyukan dake kunshe cikin kasafin kudin kasar na 2020.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.