Ba shiga ba fita a Daura- Gwamnan Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina da ke arewacin Najeriya ta kafa dokar hana shige da fice a Karamar Hukumar Daura bayan gano wasu karin mutane dauke da cutar coronavirus, lamarin da ke zuwa jim kadan da mutuwar wani likita a sanadiyar cutar.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Gwamnan jihar, Aminu Bello Masari ya ce, dokar hana shige da ficen za ta fara aiki ne daga karfe bakwai na safiyar Asabar (wato gobe) a garin na Daura bayan gano mutane uku da suka kamu da cutar.
Mutanen da aka gano sun kamu da cutar, iyalan likitan nan ne da coronavirus ta kashe shi a garin.
Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren bayanin Gwamna Aminu Bello Masari
Muryar Aminu Bello Masari kan dokar hana fita a Daura
Jim kadan da mutuwarsa ne aka yi wa iyalansa gwaji, inda sakamako ya nuna cewa, lallai sun harbu da annobar.
A cikin makon nan ne, gwamna Masari ya sanar cewa coronavirus ce ta yi ajalin likitan bayan ya dawo daga jihohin Kogi da Lagos.
A karo na farko kenan da cutar coronavirus ke kisa a Jihar Katsina.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu