Isa ga babban shafi
Najeriya

Coronavirus ta kashe likita a jihar Katsina

Wani likita a Daura da ke jihar Katsinan Najeriya ya mutu sakamakon kamuwa da cutar coronavirus, bayan ya ziyarci jihohin Kogi da Lagos.

Gwamnan jihar Katsina Amnu Bello Masari ya ce za a bi diddigin mutanen da likitan ya yi hulda da su
Gwamnan jihar Katsina Amnu Bello Masari ya ce za a bi diddigin mutanen da likitan ya yi hulda da su freedomradionig
Talla

Gwamnan Jihar Aminu Bello Masari ya sanar da mutuwarsa bayan an yi gwajin samfurin jininsa a birnin Abuja wanda ya tabbatar cewa cutar ta coronavirus ta kashe shi.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakken bayanin da gwamnan Katsina ya yi kan mutuwar likitan.

Aminu Bello Masari kan mutuwar likita a Daura bayan fama da coronavirus

Masari ya ce, tuni suka  tashi tawagar likitoci zuwa garin Daura domin bin diddigin mutanen da likitan ya yi hulda da su da zummar yi musu gwaji da kuma killace su saboda fargabar cewa, su ma sun kamu da wannan annoba.

Ana iya cewa wannan ne karo na farko da cutar coronavirus ke kisa a Jihar Katsina da ke Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.