Isa ga babban shafi
Coronavirus

Borno, Kebbi da Enugu sun kafa dokar hana shiga da fita daga cikinsu

Ganin yadda annobar coronavirus ko kuma COVID-19 ke ci gaba da yaduwa sannu a hankali zuwa sassan Najeriya, gwamnatocin jihohin kasar da dama sun soma tsaurara matakan yakar annobar.

Misalin fasalin kwayar cutar Coronavirus.
Misalin fasalin kwayar cutar Coronavirus. World Health Organization
Talla

Wasu daga cikin jihohin da a baya bayan nan suka sanar da matakan sun hada da Borno a arewa maso gabashin Najeriya, inda gwamna kuma farfesa Babagana Zulum ya haramta shiga da fita daga cikin jihar daga ranar talata 31 ga watan maris, sai dai dokar ba za ta shafi sufurin abinci da magunguna ba.

A jihar Kebbi kuwa, tun a daren jiya asabar dokar hana shiga da fita daga cikinta ta soma aiki domin dakile yaduwar annobar murar ta coronavirus.

Sai kuma jihar Enugu, inda a nan ma gwamnati ta datse iyakokinta gami da rufe kasuwanni, bayan samun mutane 2 da suka kamu da cutar, abinda ya sanya ta zama jiha ta farko a kudu maso gabashin kasar ta Najeriya da annobar ta shafa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.