Isa ga babban shafi
Coronavirus

Gwamnatin Legas ta kafa dokar hana zirga-zirga

Gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu, ya sanar da kafa dokar hana fita a daukacin jihar daga karfe takwas na dare zuwa 6 na safe.

Layin Broad, daya daga cikin yankunan dake kan gaba a birnin Legas, wajen yawan zirga-zirga saboda manyan kamfanonin dake yankin, amma annobar cornavirus ko kuma COVID-19 ta tilastawa jama'a takaita zirga-zirga.
Layin Broad, daya daga cikin yankunan dake kan gaba a birnin Legas, wajen yawan zirga-zirga saboda manyan kamfanonin dake yankin, amma annobar cornavirus ko kuma COVID-19 ta tilastawa jama'a takaita zirga-zirga. AFP Photo/PIUS UTOMI EKPEI
Talla

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin jawabi kan halin da ake ciki dangane da annobar murar coronavirus dake jihar, inda ya ce dokar hana fita za ta soma aiki daga gobe lahadi, kuma a rana za a rufe filayen jiragen saman jihar daga zirga-zirgar cikin gida tsawon mako 2.

A cewar gwamna Sanwo-Olu nan gaba kadan kuma za a iya kaiwa ga kafa dokar hana fitar ma baki daya sabanin daga dare zuwa safe, muddin aka cigaba da samun karuwar wadanda annobar ke shafa, zuwa wani adadi da bai bayyana ba.

Sanwo-Olu ya ce gwamnati za ta yi amfani da damar wajen fesa sinadaran tsaftace muhallin jama’a, wanda ta bayyana kammala shigo da injinun da za a yi amfani da su wajen aikin.

Matakin gwamnatin Legas din dai ya zo ne sa’ao’i bayanda cibiyar bincike da dakile yaduwar cutuka ta Najeriya ta sanar da karuwar wadanda suka kamu da cutar coronavirus daga 70 zuwa 81, 52 daga cikinsu kuma a birnin na Legas.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.