Isa ga babban shafi

Najeriya na farautar mutane sama da dubu 4 saboda coronavirus

Gwamnatin Najeriya tace tana neman mutane akalla 4,370 ruwa ajallo saboda zargin yin mu’amala da masu dauke da cutar coronavirus domin tantance lafiyar su.

Jami'an lafiya a kasar Senegal
Jami'an lafiya a kasar Senegal REUTERS/Zohra Bensemra
Talla

Ministan yada labarai Lai Mohammed ya sanar da wannan adadi inda ya bukaci wadanda ake nema da su gabatar da kan su cikin gaggawa ga hukumomi domin yi musu gwajin da ya kamata.

Mohammed ya bukaci hadin kan al’ummar kasar wajen wannan yaki da gwamnati ta kaddamar domin kare lafiyar jama’ar ta, wanda tuni aka fara ganin alamar samun nasara.

Ministan yace samun mai dauke da cutar ba wai an yanke masa hukuncin kisa bane, sai dai hakan zai bashi damar samun kular da ta dace domin ganin ya samu sauki.

Mista Mohammed yayi zargin cewar akwai mutanen da suka dawo daga kasashen waje amma sai suka bada adireshi da lambobin bogi abinda ya hana gano inda suke.

Ministan ya kuma bayyana damuwa kan yadda wasu mutane ke bijirewa umurnin zama a gida da aka bayar, inda yace gwamnati na nazarin tsaurara dokar da kuma shirin hana tafiye tafiye daga Jiha zuwa Jiha da kuma daga gari zuwa wani gari domin shawo kan wannan annoba da ta addabi kasashen duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.